Muna daf da hadewa da sauran jam'iyyun adawa don fatattakar 'yan maja a 2019 - PDP

Muna daf da hadewa da sauran jam'iyyun adawa don fatattakar 'yan maja a 2019 - PDP

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP Prince Uche Secondus ya shaidawa wakilin mu na kamfanin jaridar Punch cewa tuni shire-shiren hadewa da sauran jam'iyyun adawa a kasar nan domin kawar da jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2019 yayi nisa.

Shugaba Secondus ya bayyana cewa kwamitin da jam'iyyar ta kafa karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas na samun gagarumar nasara don kuwa tuni sun kai wani mataki na fahimtar juna da wasu jam'iyyun.

Muna daf da hadewa da sauran jam'iyyun adawa don fatattakar 'yan maja a 2019 - PDP

Muna daf da hadewa da sauran jam'iyyun adawa don fatattakar 'yan maja a 2019 - PDP

KU KARANTA: An samu mai mai tarin yawa a rijiyoyi 7 a Arewa

A wani labarin kuma, Wasu jami'an rundunar 'yan sanda a Najeriya dauke da muggan makamai mun samu cewa sun kutsa a gidan wani hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan dake a karamar hukumar Ese-Odo ta jihar Ondo a ranar Alhamis din da ta gabata.

'Yan sandan kamar yadda muka samu sun shiga gidan na tsohon mai baiwa shugaba Jonathan shawara ne akan lamurran 'yan Neja Delta mai suna Mista Kingsley Kuku suna harbe-harbe a sararin samaniya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel