'Yan sanda dauke da makamai sun kutsa a gidan wani hadimin tsohon shugaba Jonathan

'Yan sanda dauke da makamai sun kutsa a gidan wani hadimin tsohon shugaba Jonathan

Wasu jami'an rundunar 'yan sanda a Najeriya dauke da muggan makamai mun samu cewa sun kutsa a gidan wani hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan dake a karamar hukumar Ese-Odo ta jihar Ondo a ranar Alhamis din da ta gabata.

'Yan sandan kamar yadda muka samu sun shiga gidan na tsohon mai baiwa shugaba Jonathan shawara ne akan lamurran 'yan Neja Delta mai suna Mista Kingsley Kuku suna harbe-harbe a sararin samaniya.

'Yan sanda dauke da makamai sun kutsa a gidan wani hadimin tsohon shugaba Jonathan

'Yan sanda dauke da makamai sun kutsa a gidan wani hadimin tsohon shugaba Jonathan

KU KARANTA: Buhari yayi sabbin nade-nade 4

Legit.ng ta samu cewa wannan samamen da 'yan sandan da suka kai su 20 suka kai a garin ya jefa al'ummar cikin halin fargaba da tsoro.

Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton ba mu samu jin ta bakin jami'an hukumar rundunar ta 'yan sanda ba game da lamarin.

A wani labarin kuma, Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana cewa kawo yanzu dai jam'iyyar ba ta da wani shafaffe da mai a cikin dukkan 'yan takarkarin da ke neman tikitin ma'iyyar don karawa da shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa na 2019.

Sai dai kuma shugaban jam'iyyar ta PDP Mista Uche Secondus ya dan yi tambihi akan halayen wanda jam'iyyar za ta iya tsayar wa inda ya ce dole ne ya zamo ckikakken dan Najeriya da ya kware sosai wajen sanin kasar wanda kuma bai da bangaranci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel