Bahallatsar Shekarau da EFCC: Rashin adalcin Buhari ne – Inji magoya baya (Bidiyo)

Bahallatsar Shekarau da EFCC: Rashin adalcin Buhari ne – Inji magoya baya (Bidiyo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha tofin Allah tsine daga bakunan al’ummar jihar Kano, musamman masoya da magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Legit.ng ta ruwaito a ranar ALhamis 24 ga watan Mayu ne hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan gaban kuliya manta sabo tare da tsohon ministan kasashen waje a zamanin Jonathan, Aminu Wali da wasu mutane uku kan badakalar kudi naira miliyan dari tara da hamsin, N950m.

KU KARANTA: Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kanana da matsakaitan sana’o’i a jihar Kano

Bahallatsar Shekarau da EFCC: Rashin adalcin Buhari ne – Inji magoya baya (Bidiyo)

Masoya Shekarau

Hukumar ta bayyana ma Kotu tuhumen tuhumen da take yi ma sa tsohon gwamnan daa ciki har da zargin lakume naira miliyan ashirin da biyar, N25m daga cikin kudin, sai dai wannan lamari bai yi ma magoya bayansa dadi ba.

Daruruwan masoya Shekarau ne suka yi dafifi a gaban Kotun, inda suka gudanar da Alkunuti tare da yayyaga hotunan Buhari da tattaka shi, suna Allah wadai da shi, sa’annan wasu sun yi zargin hakan baya rasa nasaba da haushin Shekarau da Buhari ke ji.

Jama’a sun yi yawa a gaban Kotun, wanda ya kai ga sai da yansanda suka harba barkonon tsohuwa tare da harba harsashi a sama wajen tarwatsa su, a lokacin da aka fito daga Kotun.

Bahallatsar Shekarau da EFCC: Rashin adalcin Buhari ne – Inji magoya baya (Bidiyo)

Bahallatsar Shekarau da EFCC

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel