‘Dan Majalisar Kano da aka dakatar yayi nasara kan Majalisar a gaban Kotu

‘Dan Majalisar Kano da aka dakatar yayi nasara kan Majalisar a gaban Kotu

- Honarabul Abdulmumin Jibrin ya doke Majalisar Wakilai a gaban Kotu

- Kotu tace ba a bi dokar kasa wajen dakatar da shi ba a kwanakin baya

- An nemi a biya shi duk albashin da ya rasa da wasu alawus da ake biya

‘Dan Majalisar Kano da aka dakatar kwanakin baya na dogon lokaci Honarabul Abdulmumin Jibrin yayi nasara kan Majalisar a gaban babban Kotun Tarayya da ke zama a Birnin Tarayya Abuja a makon nan kamar yadda Jaridar The Cable ta bayyana.

‘Dan Majalisar Kano da aka dakatar yayi nasara kan Majalisar a gaban Kotu

Kotu tace a biya Abdulmumin Jibrin albashin sa watanni

Labari ya zo mana cewa Kotu ta nemi a biya ‘Dan Majalisar na Jam’iyyar APC da yake wakiltar Kiru da Bebeji watau Abdulmumin Jibrin duk kudin sa da ba a biya shi ba a lokacin da aka dakatar da shi na kwanaki 180 saboda tona asirin 'Yan Majalisar.

KU KARANTA: Za a mikawa Shugaban Kasa kundin kasafin kudin bana

A lokacin an dakatar da Honarabul Jibrin daga shiga Majalisar ne bayan ya bankado irin cushen da manyan ‘Yan Majalisar Tarayya ke yi cikin kundin kasafin kudin kasar wanda har ya haura na Naira Biliyan 30 wanda bayan nan ne ya garaya Kotu.

Yanzu haka dai Majalisar Wakilan ta Tarayya ta sha kashi a gaban Kotu inda aka yanke hukunci cewa tun farko Majalisar bai halatatta ta dakatar da Hon. Jibrin ba. Alkali Jon Tsoho yace Majalisa ba ta da wannan hurumi kuma a biya sa albashin na sa.

Kwanan nan dai Kotu ta sauke dakatarwar da Majalisar Dattawa tayi wa Sanata Ovie Omo-Agege. Kafin na wani Kotu da k Abuja ma dai yayi tir da dakatarwar da Majalisa tayi wa Sanata Ali Ndume.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel