Femi Adesina: Makafi ne kurum ba su ganin ayyukan alherin Buhari

Femi Adesina: Makafi ne kurum ba su ganin ayyukan alherin Buhari

- Mai magana da yawun Shugaba Buhari ya lissafo alherin Gwamnatin nan

- Femi Adesina yace komai hassadar mutum ya san cewa Buhari na kokari

- Shugaba Buhari na kokarin babbako da tattalin arzikin Najeriya a yanzu

Mun samu labari cewa mai magana da yawun bakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari watau Mista Femi Adesina yace Makafi ne kurum ba su ganin irin kokarin Gwamnatin nan ta Shugaba Buhari.

Femi Adesina: Makafi ne kurum ba su ganin ayyukan alherin Buhari

Ko ka ki Allah za kace Buhari na aiki - Femi Adesina

Mai magana da yawun Shugaban Kasa Buhari yace ‘Yan adawan wannan Gwamnati sun rantse cewa sai sun yi bakin kokarin su wajen batawa Shugaba Buhari suna ta hanyar zuzuta wasu abubuwan sharrin da ke faruwa a cikin Kasar.

Sai dai duk da haka babban Hadimin Shugaban Kasar yace an ga alheri a Gwamnatin Buhari ganin yadda alkaluman tattalin arziki su ka zabura a farkon bana. Adesina yace tsadar kayan abinci ya ragu matuka yanzu a Gwamnatin nan.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirin yin abin da ya gagari Najeriya tun 1977

Bayan nan kuma Femi Adesina ya bayyana cewa kudin kasar wajen Najeriya ya kusa shiga Dala Biliyan 50 bayan abin da tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya bari bai kai Dala Biliyan 30 ba duk da kudin da aka samu wajen man fetur.

Adesina yace wannan kadan kenan daga alheran Gwamnatin Buhari kuma komai adawar mutum ya san da wannan. Adesina yace Shugaban Kasa Buhari na kokarin habaka tattalin arzikin Kasar ne har Talaka tukuf ya ji a aljihun sa.

Kun ji cewa wata Kungiya ta Buhari Media Organization (BO) ta fadawa tsohon Shugaban Kasar nan Cif Olusegun Obasanjo ya daina wani surutu ya fito da wutan Najeriya kurum da ya batar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel