Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kanana da matsakaitan sana’o’i a jihar Kano

Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kanana da matsakaitan sana’o’i a jihar Kano

Mataimakin shugaban kasa Farfes Yemi Osinbajo ya kai ziyarar aiki na yini guda jihar Kano, inda ya halarci taron bajakolin kanana da matsakaita sanao’I karo na goma sha biyar da ya gudana a jihar.

Legit.ng ta ruwaito Osinbajo ya bayyana a yayin ziyarar cewa kanana da matsakaita sana’o’I suna samar da kashi 50 na tattalin arzikin Najeriya, wannan ne ya sanya shugaban kasa Muhamamdu Buhari jajircew wajen ganin ya habbaka sana’o’in.

KU KARANTA: Na gamsu da zaman lafiyar da aka samu a Gambia – Buhari ga jakadan Gambia

Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kanana da matsakaitan sana’o’i a jihar Kano

Mataimakin shugaban kasa

Osinbajo yace kokarin d Buhari ke yin a ganin ya taimakin masu kananan sana’o’I shi ne ta hanyar sama musu da bashin kudi mai saukin ruwa, saukaka musu hanyoyin yi ma sana’o’insu rajista, da na abubuwan da suke samarwa.

Wannan bajakoli dai ana shirya shi ne don ya kasance wata kafa da gwamnati ke ganawa da masu kananan sana’o’I don jin matsalolinsu tare da samar da hanyoyo shawo kan matsalolin, ta hanyar basu shawarwari da kuma sabbin hanyoyi gudanar da sana’o’insu na zamani.

Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kanana da matsakaitan sana’o’i a jihar Kano

Mataimakin shugaban kasa

Daga karshe Osinbajo ya kai ziyarar gani da ido zuwa babbar gadar nan dake titin Murtala Muhammed, wanda tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso ya fara, a yanzu haka gwamna Ganduje ke cigaba da ita, idan aka kammala ta zata zamo gada na kan kasa mafi tsawo a Najeriya.

Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kanana da matsakaitan sana’o’i a jihar Kano

Mataimakin shugaban kasa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel