Wani Sanatan Najeriya ya roki Minista Lai Muhammed da ya daina karya albarkacin Azumin Ramadana

Wani Sanatan Najeriya ya roki Minista Lai Muhammed da ya daina karya albarkacin Azumin Ramadana

A wani salo irin na hamayyar siyasa tsakanin manyan jam’iyyu guda biyu na Najeriya, jam’iyyar PDP da jam’iyyar APC, bangarorin biyu sun cigaba da kasancewa kishiyoyi ga juna, inda aka jiyo wani sashi na zargin wani sashi da zuki ta malle, ban kama ba, inji yara.

Legit.ng ta ruwaito ministan watsa labaru da raya al’adu, Lai Muhammed ya bayyana ma yan Najeriya cewa yana da tabbacin zasu kwarara ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ruwan kuri’u a zaben shekarar 2019

KU KARANTA: Na gamsu da zaman lafiyar da aka samu a Gambia – Buhari ga jakadan Gambia

Minista Lai ya danganta wannan tabbaci da yake da shi ne ga ikirarin da yayi na cewa gwamnatin APC ta cika ma yan Najeriya dukkanin alkawaurran da ta daukan musu, don haka zaben 2019 zai zama mai saukin lashewa ga Buhari.

Wani Sanatan Najeriya ya roki Minista Lai Muhammed da ya daina karya albarkacin Azumin Ramadana

Sanata, Lai , Reno

Sai dai ashe wannan magana na Lai Muhammed ya yi ma Sanata Ben Murrau Bruce zafi, inda yayi caraf ya yi ma Minista Lai Muhammed raddi, inda ya yi mamakin yadda Ministan ke yin karya a watan Ramadan.

“Kaico! Shin da gaske wani zai iya bugun kirji ya yi wannan magana a cikin wata mai alfarma watan Ramadan, watan da ake bukatar duk Musulmai na gaske su kasance masu gaskiya?” Inji Murray kamar yadda ya wallafa a shafinsa an Twitter.

Haka zalika shi ma hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya ja kunne Lai, inda yace: “Wa zai tuna ma Lai cewa ana cikin watan Ramadan, don haka ba abinci kadai ake daina ci ba, hatta karya ana so Musulmi ya daina. Lai kaji tsoron Allah.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel