Mun kayyade ranar mika Kasafin Kudin 2018 zuwa ga Shugaba Buhari - Saraki

Mun kayyade ranar mika Kasafin Kudin 2018 zuwa ga Shugaba Buhari - Saraki

A ranar Juma'a ta yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi idanu biyu da kasafin kudin 2018 wanda majalisar dokoki ta tarayya ta shigar da shi cikin dokar kasa a makon da ya gabata.

Shugaban Majalisar dattawa, Bukola Saraki, shine ya bayyana hakan a ranar Alhamis din da ta gabata yayin halartar liyafar buda bakin azumin ramalana tare da wasu jiga-jigan majalisa a fadar Villa ta shugaban kasa dake babban birnin tarayya.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne majalisar ta shigar da sabon kasafin kudin cikin dokar kasa bayan da shugaba Buhari ya gabatar da shi kimanin watannin bakwai da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa, a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata ne shugaba Buhari ya gabatar da kasafi na Naira Tiriliyan 8.612 inda bayan kididdigar majalisar dokoki ta sauya shi zuwa Naira Tiriliyan 9.12 tare da amincewar fadar ta shugaban kasa.

Mun kayyade ranar mika Kasafin Kudin 2018 zuwa ga Shugaba Buhari - Saraki

Mun kayyade ranar mika Kasafin Kudin 2018 zuwa ga Shugaba Buhari - Saraki
Source: Depositphotos

A yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, Saraki ya bayyana cewa an samu tsaikon mako guda na gabatar da kasafin kudin ga shugaba Buhari sakamakon banbancin lissafi tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa, wanda a halin yanzu an samu daidaito.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ya kasance Jagora mai rauni - Ben Bruce

Shugaban na majalisar dattawa ya bayar tabbacin cewa a yau Juma'a za gabatar da kasafin kudin ga shugaban kasa sakamakon amincewar majalisun biyu yayin zama da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata.

Saraki ya kuma yabawa shugaba Buhari tare da godiya a gare sa dangane da daukar nauyin liyafar buda baki a fadar sa, inda yake sa ran za a ci gaba da samun kyakkyawar alaka tsakanin shugabanci da dokokin gwamnatin Najeriya.

Kamar yadda kamfanin dillanci labarai na Najeriya ya ruwaito, majalisar ta kayyade farashin gangar man fetur daga dalar Amurka 45 zuwa Dala 50.5 a cikin kasafin kudin na bana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel