Ya kashe abokin hamayyar sa, ya datse masa yatsu ya sayar da su a kan N5,000

Ya kashe abokin hamayyar sa, ya datse masa yatsu ya sayar da su a kan N5,000

- Hukumar 'yan sanda a jihar Ogun tayi nasarar cafke wani mai laifi da ake zargi da kisan wani mai suna Shakiru tare da datse masa hannaye

- Rahotanni sun bayyana cewar, Kayode Oreneye mai shekara 27, ya kashe Shakiru tare da sayar wa wani boka tafin hannayen sa N5,000

- Kwamishinan 'yan sanda a jihar Ogun, Ahmed Iliyasu, ya gabatar da Oreneye tare wasu masu laifi 47

Hukumar 'yan sanda a jihar Ogun tayi nasarar cafke wani mai laifi da ake zargin dan kungiyar asiri ne game da kisan wani mai suna Shakiru tare da datse masa hannaye.

Rahotanni sun bayyana cewar, Kayode Oreneye mai shekara 27, ya kashe Shakiru tare da sayar wa wani boka tafin hannayen sa N5,000.

Ya kashe abokin hamayyar sa, ya datse masa yatsu ya sayar da su a kan N5,000

Dan kungiyar asiri; Oroneye

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Ogun, Ahmed Iliyasu, ya gabatar da Oreneye, dan kungiyar asiri ta Aiye, tare wasu masu laifi 47 ga manema labarai a ofishin hukumar 'yan sanda dake Eleweran a Abeokuta.

Oroneye ya shaidawa manema labarai cewar ya kashe abokin hamayyar sa, Shakiru, ne saboda ya kashe wasu 'yan kungiyar su uku tare da yunkurin kashe shi har sau uku.

DUBA WANNAN: Magoya bayan Shekarau sun sha jibga da ruwan barkonon tsohuwa

Oreneye ya kara da cewa, ya harbi Shakiru ne a kwanar Library dake Ilaro a ranar 12 ga watan Fabrairu na shekarar nan tare da bayyana cewar ya datse hannayen sa ya sayar wa da wani boka mai suna Jimoh.

Kwamishina Iliyasu ya ce sun kama maiaifin ne a wata mashaya dake kwanar Oke Ilewo a Abeokuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel