Muhimman bayanai 5 game da Musiliu Smith, sabon shugaban hukumar 'yan sanda da Buhari ya nada

Muhimman bayanai 5 game da Musiliu Smith, sabon shugaban hukumar 'yan sanda da Buhari ya nada

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon shugaban hukumar ‘yan sanda Musiliu Smith, a matsayin shugaban hukumar gudanarwar ‘yan sanda.

Shugaba Buhari ya nada Musiliu Smith a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar ‘yan Sanda Mike Okiro.

Muhimman bayanai 5 game da Musiliu Smith, sabon shugaban hukumar 'yan sanda da Buhari ya nada

Muhimman bayanai 5 game da Musiliu Smith, sabon shugaban hukumar 'yan sanda da Buhari ya nada

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi sabbin nade-nade 4

Haka ma dai shugaba Muhammadu Buhari ya nada wasu mutane biyar a matsayin mambobin hukumar gudanarwar ta ‘yan sanda.

Kamar kullum dai, Legit.ng ta zakulo maku muhimman bayanai 5 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban.

1. An haifi Alhaji Musiliu Smith ne a ranar 17 ga watan Afrilu, shekarar 1946.

2. Musiliu Smith haka kuma ya fara aikin dan sanda ne a matsayin mataimakin Sifuritanda kuma ya yi aiki a wurare da dama da suka hada da Legas, Adamawa, Kwara da kuma Ribas.

3. Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya nada shi Insifecta Janar na 'yan sandan Najeriya a shekarar 1999.

4. Cif Obasanjo har ila yau ya tsige shi a shekarar 2002.

5. A shekarar 2007 tsohon gwamnan jihar Legas Babatunde Fashola ya nada shi a matsayin shugaban majalisar koli ta tsaron jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel