Da dumin sa: 'Yan majalisa a wannan jihar sun tsige mataimakin kakakin su

Da dumin sa: 'Yan majalisa a wannan jihar sun tsige mataimakin kakakin su

Yan majalisar jahar Ekiti da ke a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a yau din nan mun samu labarin cewa sun tsige mataimakin kakakin majalisar Honorable Segun Adewumi bisa zargin sa da sukayi da aikata munanan laifuka.

Haka ma dai duk a zaman majalisar na yau, 'yan majalisar sun kuma tsige mai tsawatarwa a zauren majalisar watau Chif Whip mai suna Akinniyi Sunday tare da maye gurbin sa da Honorable Olawale Onigiobi.

Da dumin sa: 'Yan majalisa a wannan jihar sun tsige mataimakin kakakin su

Da dumin sa: 'Yan majalisa a wannan jihar sun tsige mataimakin kakakin su

KU KARANTA: Shugabannin Kiristoci a Najeriya sun ce Buhari yayi murabus

Legit.ng ta samu cewa mai magana da yawun 'yan majalisar jihar Dakta Samuel Omotoso shine ya sanar da hakan ga manema labarai inda kuma ya bayyana cewa tuni har sun maye gurbin mataimakin kakakin majalisar da Honorable Olawale Onigiobi.

A wani labarin kuma, Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN ya wanken kansa daga dukkan zargin da ake yi masa na cewa wai kungiyar ta karbi kyautar kudi daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar yayi wannan jawabin ne a ta bakin babban Sakataren ta na kasa Rabaran Dakta Adeniyi Adeyemi yayin da ake kaddamar da shugabannin kungiyar na jihar Ogun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel