Ana zargin Buhari da ba shugabannin kungiyar Kiristoci cin hanci na makudan kudade

Ana zargin Buhari da ba shugabannin kungiyar Kiristoci cin hanci na makudan kudade

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN ya wanken kansa daga dukkan zargin da ake yi masa na cewa wai kungiyar ta karbi kyautar kudi daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar yayi wannan jawabin ne a ta bakin babban Sakataren ta na kasa Rabaran Dakta Adeniyi Adeyemi yayin da ake kaddamar da shugabannin kungiyar na jihar Ogun.

Ana zargin Buhari da ba shugabannin kungiyar Kiristoci cin hanci na makudan kudade

Ana zargin Buhari da ba shugabannin kungiyar Kiristoci cin hanci na makudan kudade

KU KARANTA: Nasarari 4 da na samu tun bayan hawa na mulki - Buhari

Legit.ng ta samu cewa ya kuma ce su tun da shugaban kasar ma ya hau kan mulki kimanin shekaru uku da suka wuce bai taba basu ko da kwandala ba.

A wani labarin kuma, Yan majalisar jahar Ekiti da ke a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a yau din nan mun samu labarin cewa sun tsige mataimakin kakakin majalisar Honorable Segun Adewumi bisa zargin sa da sukayi da aikata munanan laifuka.

Haka ma dai duk a zaman majalisar na yau, 'yan majalisar sun kuma tsige mai tsawatarwa a zauren majalisar watau Chif Whip mai suna Akinniyi Sunday tare da maye gurbin sa da Honorable Olawale Onigiobi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel