Dalilin da yasa Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi yayi murabus

Dalilin da yasa Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi yayi murabus

Rahotanni dangane da dalilin da ya sanya mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Nuhu Gadado ya yi murabus a ranar Larabar da ta gabata sun bayyana kamar yadda shafin jaridar Vanguard ta bayyana.

A ranar da ta gabata ne mataimakin gwamnan ya gabatar da takardar sa ta murabus ga gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubukar, inda hadiman sa na sadarwa ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Hadimin mataimakin gwamnan, Yakubu Adamu, ya bayyana cewa ubangidan sa ya aika da takardar sa ta murabus ga gwamnan da sanadin ofishin babban sakataren gwamnatin jihar.

Cikin rubutacciyar wasikar da mataimakin gwamnan ya gabatar, Legit.ng ta fahimci cewa ya jaddada dalilin da tun a baya ya alanta bautawa jihar sa a karo guda watau shekaru hudu kenan akan karagar mulki.

Gwamnan jihar Bauchi: Muhammad Abdullahi Abubakar

Gwamnan jihar Bauchi: Muhammad Abdullahi Abubakar

Yake cewa, ya kamata ace ya ga karshen wannan karo na farko da ayyana bautawa jihar sa zuwa shekara mai gabatowa, sai dai yanayi na nauye-nauyen aiki dake kara hawa kansa ya ga kamatuwar kawo karshen hakan tun kafin lamari yayi nisa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Obasanjo na daya daga cikin mafi shahara akan Rashawa - Sagay

A sanadiyar wannan dalili ne ya sanya mataimakin gwamnan yayi murabus, inda ya tunatar da gwamnan wannan kudiri nasa na bautawa jihar a karo guda kamar yadda suka yi yarjejeniya tun a baya.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar da ta gabata gwamnan jihar ya aminta da murabus din mataimakin sa, inda ya yi jinjina a gare sa dangane da yanayi na rabuwa da kuma fatan zai amsa kiran jihar sa a duk yayin da bukata ta taso wajen sauke nauyi a karo na gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel