Gwamnatin tarayya ta ware kwanaki hudu na murnar ranar dimokradiyya

Gwamnatin tarayya ta ware kwanaki hudu na murnar ranar dimokradiyya

Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin shagulgulan biki na tsawon kwanaki hudu domin bikin murnar ranar dimokradiyya da za a fara daga gobe, Juma’a, 25 ga watan Mayu.

Daraktan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin Najeriya, Lawrence Ojabo, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fito yau, Alhamis, a Abuja.

Ya bayyana cewar za a fara bikin ranar dimokradiyyar da gudanar da addu’o’i na musamman a babban masallacin Abuja a gobe, Juma,a, 25 ga watan Mayu.

Taken bikin murnar ranar na wannan shekara shine, “inganta zaman lafiya domin samun shugabanci nagari da samun cigaba mai dorewa”.

Gwamnatin tarayya ta ware kwanaki hudu na murnar ranar dimokradiyya

Tutocin Najeriya

Kazalika za a gudanar da wasu addu’o’in na musamman ranar Lahadi a babban Cocin kasa dake cikin birnin tarayya, Abuja, ranar Lahadi.

Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Attahiru Jega, ne zai zama bako na musamman da zai gabatar da lakca, ranar Litinin, 28 ga watan Mayu, da misalign 10:00 na safe a dakin taro na kasa da kasa dake Abuja.

DUBA WANNAN: Jami'an tsaro sun jibgi wasu magoya bayan Shekarau bayan kotu ta bayar da belin sa

Mista Ojabo ya kara da cewar ana saka ran shagulgulan bikin zasu samu wakilcin masu ruwa da tsaki daga kowanne bangare na gwamnati da suka hada ‘yan majalisu, ministoci, shugabannin hukumomin gwamnati da ma jama’ar kasa.

Najeriya na bikin murnar ranar dimokradiyya duk ranar 29 ga watan Mayu na kowacce shekara domin nuna farinciki da dawwamar siyasa a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel