Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ya kasance Jagora mai rauni - Ben Bruce

Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ya kasance Jagora mai rauni - Ben Bruce

Sanata mai wakilcin mazabar jihar Bayelsa ta Gabas a majalisar dattawa, Ben Murray Bruce ya bayyana cewa, ko shakka babu shugaban kasa Muhammadu Buhari jagora ne mai matukar rauni.

Ben Murray Bruce

Ben Murray Bruce

Dan majalisar na jihar Bayelsa ya bayyana hakan ne a shafin sa na dandalin sada zumunta ta twitter a ranar Larabar da ta gabata.

Bruce ya bayyana cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta gaza wajen kammala wani muhimmin aiki da ta kaddamar a kasar nan in banda farfajiyar jirgin sama mai saukar ungulu watau helikafta a mahaifar sa ta garin Daura dake jihar Katsina.

Dattijon ya bayyana a shafin nasa cewa, duk wani jagora mai karfafaffar zuciya zai kula da al'ummar sa a maimakon kulawa da kansa.

A kalaman sa, "abin takaici ne a ce wannan gwamnati ba za ta iya haskaka wani muhimmin aiki da ta kaddamar kuma ta kammala cikin shekaru uku da ta shafe a karagar mulki in banda farfajiyar jirgin sama mai saukar ungulu a garin Daura."

KARANTA KUMA: Zambar N950m: Hukumar EFCC ta garkame Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau

"Shugaba mai rauni kadai ke kulawa da kansa a maimakon kulawa da mutanen da yake jagoranta."

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan caccaka ta zo ne a yayin da shugaban kasa Buhari ya ke neman titsiye tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo akan Dalar Amurka Biliyan 16 da ya batar a sashen wutar lantarki wanda kawowa yanzu babu amo ballantana labari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel