EFCC ta kama wasu mutane biyu akan laifin damfarar N31m

EFCC ta kama wasu mutane biyu akan laifin damfarar N31m

- Jami’an hukumar yaki da rashawa ta kama wasu mutane biyu wadanda ake zargi da damfarar wani mutum N31m da zimmar zasu yi masa kudin tsafi

- Wadanda aka kama sune Balogun Olumide Ojo da Augustine Opaso

- An kama su ne sakamakon korafi da wanda suka damfara ya kai, inda yace sun yaudareshi akan cewa zai iya samun dukiyar danginsa ta hanyar wata addu’a ta musamman da zasu yi masa

Jami’an hukumar yaki da rashawa ta kama wasu mutane biyu wadanda ake zargi da damfarar wani mutum N31m da zimmar zasuyi masa kudin tsafi.

Wadanda aka kama sune Balogun Olumide Ojo da Augustine Opaso, an kama su ne a jihar Rivers, amma kuma suna damfarar mutane har a garin Akunba dake jihar Ondo.

EFCC ta kama wasu mutane biyu akan laifin damfarar N31m

EFCC ta kama wasu mutane biyu akan laifin damfarar N31m

An kama su ne sakamakon korafi da wanda suka damfara ya kai, inda yace sun yaudareshi akan cewa zai iya samun dukiyar danginsa ta hanyar wata addu’a ta musamman da zasu yi masa, ta haka ne akayi nasarar kama daya daga cikin ‘yan damfara a Presidential Hotel dake garin Pataskum.

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Diyar sarkin Kano ta kammala karatun digiri a kasar Faransa

Ojo ya bayyana cewa suna da wani wurin bauta da suke gudanar da harkokinnsu na tsubbu a garin Akungba dake jihar Ondo, inda baya hukumar ta bincika wurin tsafin sun samu hotuna da abubuwa da dama da suke gudanar da al’amurransu na tsafi dasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel