An yi harbe-harbe a Kano bayan kotu ta bayar da belin Shekarau

An yi harbe-harbe a Kano bayan kotu ta bayar da belin Shekarau

An yi harbe-harben iska a wata kotun tarayya dake Kano inda hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, da wasu mutane biyu bisa tuhumar su da hannu cikin cin kudin makamai a matsayin na yakin neman zaben shekarar 2015.

Shekarau, Aminu Wali da Mansur Ibrahim na fuskantar caji guda 6 da suka hada da karbar kudi da adadin su ya kai miliyan N950m daga ofishin tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madueke, a matsayin kudin yakin neman zaben 2015.

A yau kotun ta bayar da belin Shekarau, Aminu Wali da Mansur Ibrahim bayan sun kwana a ofishin hukumar EFCC.

An yi harbe-harbe a Kano bayan kotu ta bayar da belin Shekarau

Magoya bayan Shekarau a harbar ofishin EFCC

Saidai an samu hatsaniya a harabar kotun yayin da magoya bayan Shekarau suka yi kokarin bankara kofar shiga kotun ba don jami’an tsaro dauke da bindigu sun shawo kan su ba.

DUBA WANNAN: Jerin jami'o'in bogi dake Najeriya

Bayan jami’an tsaro sun yi nasarar tarwatsa magoya bayan na Shekarau ne sai suka fara harbin iska tare da sakin barkonon tsohuwa, yanayin da ya saka manyan ‘yan siyasa da lauyoyi rantawa cikin na kare.

Kotun, karkashin mai shari’a Zainab B. Abubakar ta bayar da belin Shekarau, Aminu Wali, da Mansur Ibrahim a kan miliyan N100m kowanne mutum tare da gabatar da ma’aikacin gwamnatin tarayya da ya kai mukamin darekta a matsayin wanda zai tsayawa kowanne mutum guda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel