Laifin Zamba: Kotu ta garkame Ize-Iyamu a jihar Edo

Laifin Zamba: Kotu ta garkame Ize-Iyamu a jihar Edo

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin Benin na jihar Edo, ta garkame tsohon dan takarar gwamnan jihar, Fasto Ize-Iyamu da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP na jihar.

Legit.ng ta fahimci cewa, sauran wanda kotun ta bayar da umarnin garkamewa sun hadar da; Cif Dan Orbih, wani tsohon dan majalisar wakilai, Mista Lucky Imasuen, Tony Azegbemi da Efe Anthony a hukumar ta EFCC.

Ize Iyamu

Ize Iyamu

Jaridar ta ruwaito cewa, za su ci gaba da baiwa diga-digan su hutu a gidan wakafi zuwa wasu lokuta da za su cika sharuddan beli.

KARANTA KUMA: Wata Mata ta yanki Tikitin Shekaru 15 a gidan Kaso da laifin yiwa wani Yaro Fyade

A ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da wadannan jiga-jigan na jihar Edo da laifin zambar makudan kudi na kimanin Naira miliyan 700.

Alkalin Kotun Mai Shari'a P. I Adjokwu, ya toshe kunnuwan sa wajen sauraron roko na lauya mai kare su, Charles Edosomwan, inda ya bayar da umarni ga hukumar ta EFCC ta tsare su a katarar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel