Fadar shugaban kasa bata sanya hannu a kwamitin APC ba - Adesina

Fadar shugaban kasa bata sanya hannu a kwamitin APC ba - Adesina

- Fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, tace babu wani kamshin gaskiya a cikin zargin da akeyi na cewa ta musanya wasu daga cikin ‘yan kwamitin taron jam’iyyar APC na kasa

- Babban mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin sadarwa Femi Adesina, ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ga manema labarai a birnin tarayya

- Adesina yace ba halin shugaba Muhammadu Buhari bane sanya baki a cikin al’amurran jam’iyya ba ko kuma lamurran da suka shafi kotu ba

A ranar Alhamis, 24 ga watan Mayu, fadar shugaban kasa tace babu wani kamshin gaskiya a cikin zargin da akeyi na cewa ta musanya wasu daga cikin ‘yan kwamitin taron jam’iyyar APC na kasa.

Babban mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin sadarwa Femi Adesina, ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ga manema labarai a birnin tarayya.

Adesina yace ba halin shugaba Muhammadu Buhari bane sanya baki a cikin al’amurran jam’iyya ba ko kuma lamurran da suka shafi kotu ba.

Fadar shugaban kasa bata sanya hannu a kwamitin APC ba - Adesina

Fadar shugaban kasa bata sanya hannu a kwamitin APC ba - Adesina

Hatsaniya ya faru a helikwatar jam’iyyar APC a birnin tarayya, a ranar Laraba, inda wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar suka gudanar da zanga-zanga akan cewa an cire sunayensu daga cikin mambobin kananan kwamitocin jam’iyyar na taron kasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu na neman shugaban kamfanin motan Innoson ruwa a jallo

A kalla mutane 50 ne wadanda sukayi ikirarin an bayyana sunayensu a kafar sadarwa a matsayin mambobin kananan kwamitocin jam’iyyar sunce an fitar da sunayensu daga jerin sunayen da aka sake fitarwa daga ofishin shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel