Na gamsu da zaman lafiyar da aka samu a Gambia – Buhari ga jakadan Gambia

Na gamsu da zaman lafiyar da aka samu a Gambia – Buhari ga jakadan Gambia

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi takardar fara aiki daga sabbin jakadun kasar Congo da na Gambia a fadar Aso Rock dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis 24 ga watan Mayu.

A yayin tarbar jakadun biyu da suka hada da Jacques Obindza na kasar Congo da Amadou Taal na kasar Gambia, Buhari ya yaba da zaman lafiya tare da kwanciyar hankalin da ya dawo kasar Gambia, biyo bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Yahaya Jammeh.

KU KARANTA: Idanun wata Mata sun yi zuru zuru bayan ta yi ma kawarta wanka da tafasashshen ruwan barkono

“Ina taya gwamnatinku murnar zaman lafiyan da aka samu a kasar, na yi farin ciki matuka da nag a komai na tafiya yadda ya kamata a kasar, haka zalika ina alfahari da rawar da Najeriya ta taka a wannan yanayi.” Inji Buhari.

Na gamsu da zaman lafiyar da aka samu a Gambia – Buhari ga jakadan Gambia

Buhari da jakadan Congo

Da yake nas jawabin, Jakadan kasar Gambi a Najeriya, Amadou Taala yace kasar Gambia na alfahari da Buhari, da kasar Najeriya gaba daya bisa rawar da suka taka wajen kawo sauyi a kasar Gambia.

“Mun yi farin ciki da kokarin da ka yi wajen kawo zaman lafiya a kasarmu, shugabanmu na ganin kimarka matuka. Kuma yana gaisheka” Inji shi.

Na gamsu da zaman lafiyar da aka samu a Gambia – Buhari ga jakadan Gambia

Buhari ga jakadan Gambia

Haka zalika shugaba Buhari ya bayyana ma jakadan kasar Congo Jacques cewa akwai bukatar a sake duba danagantakar diflomasiyya dake tsakanin Najeriya da Congo, musamman ta bangaren kasuwanci.

Sai dai Jakada Jacques yace zai yi iya bakin kokarinsa na ganin an inganta alakar cinikayya tsakanin Najeriya da Congo, har ma ya kara da cewa a yanzu haka Dangote da wasu manyan bankunan Najeriya sun bude kamfanoni a kasar Congo.

Na gamsu da zaman lafiyar da aka samu a Gambia – Buhari ga jakadan Gambia

Jakadun

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel