Jerin wasu Jihohin Najeriya da ke cin ribar sabon tsarin Gwamnatin Buhari

Jerin wasu Jihohin Najeriya da ke cin ribar sabon tsarin Gwamnatin Buhari

Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta kawo wani tsari na ciyar da abinci ga Kananan Yara da ke Makarantun Firamare a wasu Jihohin Kasar. Hakan ya taimaka wajen samun karuwar masu shiga Makarantar Boko a Najeriya.

Jerin wasu Jihohin Najeriya da ke cin ribar sabon tsarin Gwamnatin Buhari

Ana ba 'Dalibai abinci kyauta a Makarantun Gwamnati

A baya kun ji yadda wannan tsari yake taimakawa Iyaye bayan kuma dinbin aikin da yayi sanadiyyar samawa Manoma da Masu dafa abinci da Direbobi da sauran su. Yaran Makarantar kuma sun kara samun lafiya da karfin karatu.

KU KARANTA: Dalilin mu na kin rage yawan ruwan da ke cikin bashin mu - CBN

A baya dai Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Jihohi 19 ke amfanuwa da wannan tsari. Yanzu abin har ta kai Jihohi 24 na kasar su na cin moriyar wannan tsari. Ga dai jerin wadannan Jihohi nan:

1. Anambra

2. Enugu

3. Oyo

4. Osun

5. Ogun

6. Ebonyi

7. Zamfara

8. Delta

9. Abia

10. Benue

11. Plateau

12. Bauchi

13. Taraba,

14. Kaduna

15. Akwa-Ibom

16. Cross River

17. Imo

18. Jigawa

19. Niger

20. Kano

21. Katsina

22. Gombe

23. Ondo da kuma Jihar

24. Borno.

Sama da Yara Miliyan 5 ake ba abinci gangariya a Makarantun Firamare na Gwamnati a wadannan Jihohi. Bayan nan Gwamnatin ta Buhari ta na kuma biyan wadanda su ka tagayyara kudi har N5000 a kowane wata domin inganta rayuwar su.

Idan ba ku manta ba a farkon 2016 Gwamnatin Jihar Kaduna ta rika ba ‘Daliban da ke aji 4-6 wanda sun haura miliyan 1.5 abinci a wajen karatu. Wannan dai ya sa an samu karuwar ‘daliban Makaranta a Jihohin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel