Karshen tika tika tik! Mutane 9 na hallaka a shekara daya – Inji wani dan Kungiyar asiri da ya shiga hannu

Karshen tika tika tik! Mutane 9 na hallaka a shekara daya – Inji wani dan Kungiyar asiri da ya shiga hannu

Rundunar Yansandan jihar Ogun sun samu nasarar cafke wani gawurtaccen matashi dake jagorantar wata kungiyar asiri, wanda shi da yaransa suka addabi al’ummar garin Abekuta, babban birnin jihar Ogun, kamar yadda jaridar Daily Independent ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunan wannan mamugunci a matsayin Gbenga Ogunsanya, kuma shekarunsa 22, hakazalika ya tabbatar da cewar ya kashe mutane tara tun daga shigarsa kungiyar a watan Maris na 2017 zuwa Mayun 2018.

KU KARANTA: Kamfanoni 27 da suka yi watanda da kudin kwangilar aikin wutar lantarki a zamanin Obasanjo

Tun a baya ne kwamishinan Yansandan jihar Ogun, Ahmed Iliyas ya sanya Ogunsanya a cikin jerin miyagun mutane 48 da rundunar ke nema ruwa a jallo, wannan ne ya sanya jami’an Yansandan farautarsam har sai da suka samu galaba akansa.

Karshen tika tika tik! Mutane 9 na hallaka a shekara daya – Inji wani dan Kungiyar asiri da ya shiga hannu

Dan kungiyar asiri

Kwamishinan Yansanda Ahmed Iliyas ya bayyana cewa Ogunsanya ne mutum mafi hadari a cikin yayan kungiyar asiri dake jihar, duba da yadda ya zama shugaban kungiyar cikin kankanin lokaci.

A wani labarin kuma, Yansandan Najeriya sun samu nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane su 14 dake addabar hanyar Kaduna zuwa Kano, inda ta gano bindigu da alburusai daga wajensu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel