Abin kwaikwayo ne: An sace sandan ikon majalisar Jihar Gombe

Abin kwaikwayo ne: An sace sandan ikon majalisar Jihar Gombe

An sace sandan majalisar jihar Gombe yayin da ake wata zama don tsige shugaba marsa rinjaye na majalisar.

Rahottani sunce shugaban marasa rinjayen, Mohammed Usman Haruna ya kira wata taron manema labarai a ranar 5 ga watan Mayu bayan kammala taron gundumarsa inda ya yi Allah wadai da yadda aka gudanar da taron.

Bayan hakan ne, sauran mambobin jam'iyyar PDP wanda su ke da rinjaye a majalisar suka fara shirye-shiryen tsige shi saboda kalaman da ya furta a taron manema labaran da ya kira baiyi musu dadi ba.

A lokacin da ake gudanar da zaman tsige shi, mutane biyar cikin mambobi takwas sun saka hannu inda suka goyi bayan tsige shi.

Abin kwaikwayo ne: An sace sandan ikon majaliisar Jihar Gombe

Abin kwaikwayo ne: An sace sandan ikon majaliisar Jihar Gombe

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Kotu ta bayar da belin Sanata Jonah Jang

Sai dai an gano daya daga cikinsu ya saka hannu a wurare biyu na goyon bayan tsigewar da akasin haka, da aka tambaya dalilin da yasa yayi hakan sai ya ce: "Tilasta mani akayi na saka hannu don amincewa da tsige shi."

Hakan yasa zaman majalisar ya hargitse tunda kawunan mambobin ya rabu gida biyu a kan batun tsige shugaban marasa rinjayen.

Hakan ya janyo daya daga cikin mambobin majalisar, Abdullahi Abubukar, mai wakiltan Akko ta Yamma ya sace sandan majalisar da misalin karfe 1.12 na ranar yau.

Wani dan majalisar mai suna Mohammed Bello daga mai wakiltan kudancin Gombe ya taimakawa Abubakar wajen tserewa da sandan majalisar kamar yadda Voice of Nigeria ta ruwaito.

Mahukuntan majalisar ba su ce komai ga yan jarida game da batun ba har yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel