Yanzu-yanzu: Bayan Koriya ta lalata masana'antar nukiliyar, Trump ya janye daga ganawa da Kim Jong Un

Yanzu-yanzu: Bayan Koriya ta lalata masana'antar nukiliyar, Trump ya janye daga ganawa da Kim Jong Un

Shugaban kasan Amurka, Donald J Trump ya alanta soke zamansa da ake sa rai da shugaban kasan Koriya ta Arewa, Kim Jong-un.

Trump ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya soke taron shine kuri da barazanar da Koriya Ta Arewa kwanakin bayan na cewa za ta soke ganawar sulhu da Amurka.

Donald Trump ya aikawa takwaransa na Koriya Ta Arewa wasika domin bayyana aniyarsa.

Ga wasikar:

Mista Trump ya ce bai dace a yi taron ba a wannan lokaci, wanda aka shirya yin sa ranar 12 ga watan Yuni a kasar Singapore.

An shirya ganawar shugaban kasar Amurka da na Koriya ta Arewa ne ranan 12 ga watan Yuni a kasar Singapore, amma Trump ya janye a yau bayan koriya ta Arewa ta lalata masana'antar kera makaman nukiliyanta.

Hakazalika, shugaban kasan Koriya ta kudu Moon Jan ae ya gana da Trump a makon nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel