Shugaba Buhari ya yi alkawarin ba zai yi katsalandan cikin harkokin jam'iyyar APC ba

Shugaba Buhari ya yi alkawarin ba zai yi katsalandan cikin harkokin jam'iyyar APC ba

- Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cewa shugaba Buhari ya sauya wasu mambobin kwamitin shirya taron APC na kasa

- Hadimin shugaban kasa ta fannin yada labarai, Femi Adesina ya ce ko kadan babu kanshin gaskiya a zancen

- Adesina ya ce ba halayan shugaban kasan bane yin katsalandan cikin harkokin jam'iiyar ko saba dokokinta

Fadar shugaban kasa ta sake jadada cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi amfani da matsayayinsa ba wajen yin katsalandan a cikin al'amuran cikin gida na jam'iyyar sa ta APC ko wasu lamaran da ke gaban kotu.

Mai bawa shugaban kasa na musamman a fani kafafen yadda labarai, Femi Adesina ne ya bayar da sanarwar a yau Alhamis.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin ba zai yi katsalandan cikin harkakin jam'iyyar APC ba

Shugaba Buhari ya yi alkawarin ba zai yi katsalandan cikin harkakin jam'iyyar APC ba

Hadimin shugaban kasar ya ce babu kanshin gaskiya a batun da wasu kafafe yadda labarai ke yadawa na cewa shugaban kasan ya sauya mambobin karamin kwamitin shirya babban taron kasa na jam'iyyar.

KU KARANTA: Gwamnatin shugaba Buhari za ta gina layin dogo da zai sada wasu jihohin Najeriya da Jamhuriyar Nijar

"Babu gaskiya cikin rahoton da wasu kafafen yadda labarai ke yadawa na cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sauya wasu ko shigar da sabbin sunaye mutane cikin kwamitin shirya taron kasa na jam'iyyar APC." inji shi.

A cewar Adesina, ya kamata duk wani dan Najeriya mai lura da yadda shugaba Buhari ya ke gudanar da al'amuransa ya gane cewa baya halin shugaba Buhari ba ne tsoma hannunsa cikin harkokin cikin gida na jam'iyya bale sabawa dokokin kundin tsarin jam'iyyarsa.

Adesina ya cigaba da cewa wasu masu son kitsa makirci ne kawai suke yadda labarin domin shugaba kasan ba zai taba aikata wani abu da ya yi kama da babakere kan lamuran jam'iyyar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel