CBN: Dalilan da yasa bamu rage yawan farashin kudin ruwa ba

CBN: Dalilan da yasa bamu rage yawan farashin kudin ruwa ba

Kwamitin dokar kudi wato Monetary Policy Committee (MPC) a turance wacce ke karkashin babban bankin Najeriya (CBN) ya tashi daga taron shi na biyu na shekara, a inda yake nuna cewa rashin zartar da kasafin kudi na shekarar 2018 da wuri zai iya jawo faduwar darajar kudin kasar in har ba a dau hukuncin gaggawa ba

CBN: Dalilan da yasa bamu rage yawan farashin kudin ruwa ba

CBN: Dalilan da yasa bamu rage yawan farashin kudin ruwa ba
Source: Depositphotos

Kwamitin dokar kudi wato Monetary Policy Committee (MPC) a turance wacce ke karkashin babban bankin Najeriya (CBN) ya tashi daga taron shi na biyu na shekara, a inda yake nuna cewa rashin zartar da kasafin kudi na shekarar 2018 da wuri zai iya jawo faduwar darajar kudin kasar in har ba a dau hukuncin gaggawa ba.

DUBA WANNAN: Trump barawo ne, makaryaci, mayaudari - inji Amurkawa

Shugaban babban bankin, Mista Godwin Emefiele wanda ya tattauna da manema labarai akan sakamakon taron yace takwas daga cikin mutane tara da suka zauna taron sun goyi bayan a bar farashin dokar kudi a kashi 14 cikin dari, rarar kudi kuma a kashi 22.5 a cikin dari, liquidity ratio a kashi 30 cikin dari sai kuma asymmetric corridor a +200-500.

Emefiele ya bayyana cewa MPC dai a baya tace matukar darajar kudi ta kara yin kasa, tabbas zata saukar da farashin dokar kudi na MPR.

Kamar yanda hukumar hasashe ta kasa wato National Bureau of Statistics (NBS) ta fadi, darajar kudin Najeriya ta kai ga kashi 12.48 cikin dari a watan Afirilu daga 13.34 cikin dari na watan Maris.

Yace MPC sunki saukar da farashin kudin MPR ne don gujewa karin faduwar darajar kudi wanda rashin zartar da kasafin 2018 da wuri da kuma zabe zai iya jawowa tattalin arzikin kasar.

"Da gaske ne munce sai darajar kudi ta karu sannan zamu rage yawan kudin ruwa, amma a bayanin mu mun nuna yanda zamu karo kudin da zamu dinga samu, daga farkon watan Mayu ko yuni na wannan shekarar. A wannan lokacin fa mu kan kasafin kudi na shekarar 2017 ne; zamu fara amfani da kasafin kudin 2018 ne a watan yuni ko yuli, za a kuma samu kasuwar kashe kudade kuma muna tsammanin kashe kudade don shirya zabe."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel