A ranar 14 ga watan yuli za’ayi jana’izar PDP a jihar Ekiti - Dan majalisa

A ranar 14 ga watan yuli za’ayi jana’izar PDP a jihar Ekiti - Dan majalisa

- Shugaban marasa rinjaye a majalisar jihar Ekiti Hon. Gboyega Aribisogan, yace APC zatayi murnar mutuwar PDP a ranar zabe bayan an kayar da ita zabe

- Dan majalisar ya bayyana PDP a matsayin mara lafiya dake kwance a kan gadon asibiti wanda baya sa ran warkewa, wanda ya san kawai mutuwa zayayi sakamakon raunukan da yayiwa kansa

- Yace PDP kamar mara lafiya ne dake ta kai kawo a kan hanya da munanan raunuka a jikinsa da cituttuka a jikinsa wanda babu wani magani ko dabara da zata hanata mutuwa a ranar 14 ga watan Yuli

Shugaban marasa rinjaye a majalisar jihar Ekiti Hon. Gboyega Aribisogan, yace APC zatayi murnar mutuwar PDP a ranar zabe bayan an kayar da ita zabe.

Dan majalisar lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar da shuwagabannin jam’iyyar suka yi, ya bayyana PDP a matsayin mara lafiya dake kwance a kan gadon asibiti wanda baya sa ran warkewa, wanda ya san kawai mutuwa zayayi sakamakon raunukan da yayiwa kansa.

A ranar 14 ga watan yuli za’ayi jana’izar PDP a jihar Ekiti - Dan majalisa

A ranar 14 ga watan yuli za’ayi jana’izar PDP a jihar Ekiti - Dan majalisa

Yace “PDP kamar mara lafiya ne dake ta kai kawo a kan hanya da munanan raunuka a jikinsa da cituttuka a jikinsa wanda babu wani magani ko dabara da zata hanata mutuwa a ranar 14 ga watan Yuli.

“Sun yanke shawarar dawo da martaba, da daraja da kuma rashin son kai na jihar. Sun yanke hukuncin magance yunwa a jihar wadda PDP ta kawowa jihar ta Ekiti a cikin shekaru hudu da suka gabata.

"Babu wata guguwar da zata canza guguwar canji wadda ke kadawa a halin yanzu.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Shugabar ma’aikata ta tarayya na kokarin kara albashin ma’aikata don inganta ayyukan gwamnati

"APC itace gwamnatin ceto ga jihar Ekiti kuma zata karasa mamaye jihar zuwa watan Oktoba na wannan shekarar”, inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel