Wata ma'aikata a Najeriya ta tilastawa ma'aikatan ta biyan kudin ID Card

Wata ma'aikata a Najeriya ta tilastawa ma'aikatan ta biyan kudin ID Card

Cibiyar fasahar tauraron dan Adam ta Najeriya, wato National Space Research and Development Agency NARSDA a turance ta ba wa ma'aikatan ta umarnin biyan kudin ID Card

Wata ma'aikata a Najeriya ta tilastawa ma'aikatan ta biyan kudin ID Card

Wata ma'aikata a Najeriya ta tilastawa ma'aikatan ta biyan kudin ID Card

Cibiyar fasahar tauraron dan Adam ta Najeriya, wato National Space Research and Development Agency NARSDA a turance ta ba wa ma'aikatan ta umarnin biyan kudin ID Card.

A wata takarda da suka manna a allon sanarwa na cibiyar, ana umartar ma'aikatan dasu dinga biyan kudin katin shaidar su sakamakon rashin isassun kudi a ma'aikatar.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa bata kama gwamnan jihar Rivers ba

A takardar da suka manna mai lamba: CSTD/ADM/41, mai kwanan wata 21 ga watan Mayu, 2018 ta kunshi sa hannun Mista Shu'aibu A. O, mataimakin darakta a maimakon daraktan cibiyar Dr. Spencer Onuh. Ga abinda wasikar ta kunsa: An umarce ni da in sanar da dukkan ma'aikatan CSTD cewar a halin yanzu babu wadataccen kudi a cibiyar nan, wanda har zata iya yiwa ma'aikatan ta ID Card. A sakamakon haka ne ake umartar ma'aikatan dasu dinga biyan kudin ID Card din su ta AP & D daga yanzu.

A rahoton da muka samu ya nuna cewa cibiyar tana da ma'aikata kasa da 500.

Kamar yanda Mr Gbenga Omole ya fada, mai aikin buga ID Card a Area 10 Abuja. " Naira 200 ne kacal kudin buga ID Card din na roba, in ma kana so da yawa zamu iya yi maka ragi."

Wani ma'aikaci da ya bukaci a rufe sunan shi ya fada mana cewa ai ma'aikata sun dade suna biyan kudin ID Card sama da shekaru biyu.

"Ai wannan ya dade yana faruwa. Da kaina na biya kudin ID Card. Abin mamaki ne ai, tunda cibiyar ba kowa zata iya yiwa ID Card a lokaci daya ba. Ma'aikatan da suka samu karin girma kadai ake ma ID Card."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel