Barin zance: Alkali ya umarci wasu ‘yan Jarida su bayyana a Kotu bayan sun tsoma bakin a shari’ar Metuh

Barin zance: Alkali ya umarci wasu ‘yan Jarida su bayyana a Kotu bayan sun tsoma bakin a shari’ar Metuh

- Azarbabi na menan kaiwa ya baro wasu 'yan Jarida

- 'Yan Jaridar dai sun yiwa Kotu shisshigi ne a wata shari'a da bata kai ga kammalawa ba

- Kuma dama idan Magana na gaban Kotu ba'a tsoma ba har sai an kammala

Sakamakon tsoma baki cikin shari’ar da har yanzu ba’a kai ga yanke hukunci ba, Alkalin babbar kotun birnin tarayya Abuja a aik da sammaci a yau Laraba ga wasu ‘yan Jarida biyu na gidan Talabijin din Channels.

Barin zance: Alkali ya umarci wasu ‘yan Jarida su bayyana a Kotu bayan sun tsoma bakin a shari’ar Metuh

Barin zance: Alkali ya umarci wasu ‘yan Jarida su bayyana a Kotu bayan sun tsoma bakin a shari’ar Metuh

Mai shari’ar da yake sauraron karar da aka kai tsohon sakataran yada labarai na jam’iyyar PDP Olisah Metuh, ya aike da sammacin ne ga wani mai gabatar da shirin da akewa lakabi da Sunrise Daily mai suna Maupe Ogun Yusuf tare da Manajan shirye-shirye Steve Judo, sakamakon tsoma baki cikin shari’ar tuhumar cin hanci da rashawa da ake yi wadda ba’a kai ga zartar da hukunci ba.

Alkalin mai suna Okon Abang ya ce su biyun su bayyana a harabar Kotun ranar 25 ga watan Mayu.

Kotun dai ta cigaba da sauraron shari’ar da ake yiwa Metuh duk da cewa ba zai halarta ba sakamakon faduwa da yayi a zaman kotun da ya gabata ranar Litinin.

KU KARANTA: 2019: Duk wani mai sha'awar takara ya aijye aikinsa kafin 29 ga watan Mayu - Gwamna Ortom

Tun bayan faduwarsa ne kuma bai kara halartar zaman kotun ranar Talata da Laraba ba amma mai shari’ar ya cigaba da sauraron karar domin Kotun na da ikon yin hakan bisa ikon da sashi na 266(a) da na 352(4) suka bata.

Mai shari’ar ya ce tun farko laifin Olisa Metuh ne tun da sai da ya umarce shi da ya cigaba da zama a kan kujerar da ake tura sa amma yaki, ya mike da nufin shi sai ya shiga cikin akwakun da ake tsayawa.

Barin zance: Alkali ya umarci wasu ‘yan Jarida su bayyana a Kotu bayan sun tsoma bakin a shari’ar Metuh

Barin zance: Alkali ya umarci wasu ‘yan Jarida su bayyana a Kotu bayan sun tsoma bakin a shari’ar Metuh

Kuma bayan faduwarsa ne ya rika kwakwazo yana ihu tare da kwaroroto da hakan ya hana cigaba da shari’ar, kuma ya jawo hankalin Mutane wurinsa sakamakon ihun da yake yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel