BMO ta mayarwa kungiyar arewa martani na cewa babu makawa Buhari ya cancanci tsayawa takara a shekarar 2019

BMO ta mayarwa kungiyar arewa martani na cewa babu makawa Buhari ya cancanci tsayawa takara a shekarar 2019

- Kungiyar sadarwa ta Buhari (BMO) ta fadawa kungiyar arewa cewa shawarar data bawa shugaban Muhammadu Buhari na kada ya tsaya takara 2019 ba shawara bace

- Ciyaman na kungiyar Austine Braimoh da kuma sakataren kungiyar Cassidy Madueke, sun ce kungiyar matsan arewa bata da hurumin hana wani tsayawa takara tinda doka bata hana shi ba

- Kungiyar ta BMO ta shawarci kungiyar ta arewa akan cewa shugaba Buhari ba shine makasudin wata matsala dake damun Najeriya ba

Kungiyar sadarwa ta Buhari (BMO) ta fadawa kungiyar arewa cewa shawarar data bawa shugaban Muhammadu Buhari na kada ya tsaya takara 2019 ba shawara bace da za’a karba.

Ciyaman na kungiyar Austine Braimoh da kuma sakataren kungiyar Cassidy Madueke, sun ce matsayin kungiyar matasan arewa bata da hurumin hana wani tsayawa takara tinda babu inda dokar ta hana shi sake tsayawa takarar a karo na biyu.

BMO ta mayarwa kungiyar arewa martani na cewa babu makawa Buhari ya cancanci tsayawa takara a shekarar 2019

BMO ta mayarwa kungiyar arewa martani na cewa babu makawa Buhari ya cancanci tsayawa takara a shekarar 2019

Kungiyar ta BMO ta shawarci kungiyar ta arewa akan cewa shugaba Buhari ba shine makasudin wata matsala dake damun Najeriya ba, sai dai ma yaki da yake yi da cin hanci da rashawa da kuma wasu matsaloli da suka hana kasar cigaba.

KU KARANTA KUMA: Za a rusa gidajen karuwai da na barasa a jihar Borno

Kungiyar ta BMO ta jawo hankalin kungiyar ta arewa akan wasu muhimman ayyuka da shugaba Buhari ya fara aiwatarwa a kasar na cigaba musamman na hanyoyin jirgin kasa, da na motoci da kuma fannin wutar lantarki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel