Za a rusa gidajen karuwai da na barasa a jihar Borno

Za a rusa gidajen karuwai da na barasa a jihar Borno

Gwamnatin Jihar Borno karkasin jagorancin Kashim Shettima, ta bada wa'adin kwanaki 10 da a rusa gidan karuwai da wajen holewanan na Galadima dake garin Maiduguri.

Galadima mattatara ce ta karuwai, mashaya da sauran lalatattu masu aikata ayyukan alfahasha da bata tarbiyar al'umma.

Hakazalika manyan Malaman musulunci na jihar sun sha jan hankalin gwamnati dangane da wannan wuri.

Wannan umurnin na zuwa ne yan kwanaki kadan bayan da Gwamna Shettima ya bada dokar korar 'yan cacar NAIJABET a fadin jiharsa.

Za a rusa gidajen karuwai da na barasa a jihar Borno

Za a rusa gidajen karuwai da na barasa a jihar Borno

A wani lamari na daban, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kawo wani tsari na biyan wadanda su ka fi kowa galabaita a Kasar nan kudi har N5000 a kowane wata domin raba su da matsi kamar yadda yayi alkawari.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa bata kama gwamnan jihar Rivers ba Read

Mun samu labari daga wata Jami’ar wannan tsari na Gwamnatin nan cewa sama da mutane 14, 000 ne ke karbar kudin da Gwamnatin nan ta Shugaba Muhammadu Buhari ta ke biyan wadanda su ka fi kowa tagayarra a cikin Jihar Kwara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel