Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa bata kama gwamnan jihar Rivers ba

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa bata kama gwamnan jihar Rivers ba

A ranar larabar nan ne ministan yada labarai na kasa, Lai Mohammed, yace da tuni gwamnatin tarayya ta kama gwamnan jihar Rivers, inda badan daga mishi kafa da gwamnati take yi ba, saboda yana a matsayin gwamnan jiha

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa bata kama gwamnan jihar Rivers ba

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa bata kama gwamnan jihar Rivers ba

A ranar larabar nan ne ministan yada labarai na kasa, Lai Mohammed, yace da tuni gwamnatin tarayya ta kama gwamnan jihar Rivers, inda badan daga mishi kafa da gwamnati take yi ba, saboda yana a matsayin gwamnan jiha. Ministan ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, bayan kammala taron mako da majalisar tarayya ta gabatar akan ikirarin da Wike yayi na cewar gwamnatin tarayya ta so ta kashe shi.

DUBA WANNAN: Jerin mutanen da zasu gwabza da Tambuwal takarar kujerar gwamnan Sokoto

Ministan yace, kawai yana cin albarkacin kujerar shi ne, amma da tuni an jima da kama shi domin aji dalilin da yasa yayi wancan ikirarin.

"Game da batun da Gwamnan jihar ta Rivers din ya bayar na cewa ya samu bayanin cewar gwamnatin tarayya tana ta shirin kashe shi a wajen taro, ina ganin daya daga cikin muhimman jin dadi shine mutum ya zama gwamna, saboda wannan kujerar tashi zata bashi kariya daga dukkan wata tuhuma.

"Bazan manta ba a wata shekara na taba yin irin wannan zargin, inda cikin gaggawa hukumar bincike ta bukaci ganina," inji Lai Mohammed.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel