Rigima na nan kwance a Jam’iyyar APC saboda zaben shugabanni

Rigima na nan kwance a Jam’iyyar APC saboda zaben shugabanni

Wata sabuwar rigima ce za ta kaure a Jam’iyyar APC a dalilin shirin zaben shugabannin Jam’iyyar da ake shirin yi. Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto wannan labari inda tace an canza sunan wadanda za su yi aikin zaben Jam’iyyar.

Rigima na nan kwance a Jam’iyyar APC saboda zaben shugabanni

Wutan wani danyen rikici na nema ya huru a cikin APC da Yan nPDP

Wasu daga cikin uwar kwamitin da za su ja ragamar zaben shugabannin Jam’iyyar na kasa da za ayi nan gaba sun koka da cewa sabon jerin sunayen da aka fito da su na kananan kwamiti inda su ke kukan cewa an cire sunayen wasu jama’an.

Sabon jerin da aka fito da shi ya taba musamman tsofaffin ‘Yan PDP da ke cikin Jam’iyyar APC yanzu. Rahoton da mu ka samu na cewa an cire sunayen wasu daga cikin ‘Yan nPDP a jerin wadanda za su yi aiki a kananan kwamiti a zaben.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Bauchi ya rasa Mataimakin sa

Majiyar ta bayyana mana cewa wadanda abin ya shafa sam ba su ji dadi ba inda aka hange su sun yi zugum a lokacin da ake rantsar da ‘Yan kwamitin a jiya. Wadanda abin ya shafa sun zargi Fadar Shugaban Kasa da wannan ‘danyen aiki.

Wani daga cikin wadanda aka goge sunan sa ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa ana zargin wata Mata ce daga Fadar Shugaban kasar ta aiko sunayen wasu mutane 50 dabam don haka aka cire sunayen su bayan a da can su na cikin jerin da aka fitar.

Tun ba yau ba wasu dama na kukan ba ayi da su a APC. Ana dai sai rai a karshen Watan Yuni a gudanar da zaben Shugabannin APC na kasa baki daya. Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar zai yi wannan aiki kuma yace ba za a kashe kudin hauka ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel