Zazzafan martini ga Obasanjo: Gwamnatinka na daga cikin waddatafi cin hanci da rashawa - Sagay

Zazzafan martini ga Obasanjo: Gwamnatinka na daga cikin waddatafi cin hanci da rashawa - Sagay

- Obasanjo ba shi da kimar da zai na fadin maganganu barkatai don shima akwai kashi a gindinsa

- Wani babban masanin shari'a da yake bawa shugaba Buhari shawara ne ya fadi haka

- Kura dai ta fara yamutsa hazo ne bayan da Buhari yayi korafin an kashe kudade masu yawa amma ba'a gani a kasa ba kan wutar lantarki

Shugaban kwamitin dake bawa shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa (PACAC) Farfesa Itse Sagay (SAN), ya bayyana cewa Gwamnatin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya jagoranta na daya daga cikin wadda tayi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.

Zazzafan martini ga Obasanjo: Gwamnatinka na daga cikin waddatafi cin hanci da rashawa - Sagay

Zazzafan martini ga Obasanjo: Gwamnatinka na daga cikin waddatafi cin hanci da rashawa - Sagay

Ya ce abin mamaki ne yadda Obasanjo yake magana sai ka ce wani mai tsarki bayan kuma duk ga kashi a jikinsa.

Maganar gaskiya, ina ga shugaban kasa Muhammadu Buhari yana dagawa tsofaffin shugabanni kafa saboda baya son ya kunya ta su bayan sun gama mulki, amma ni ina ganin lallai ya kamata a binciki yadda Obasanjo ya kashe har $16b wajen samar da wutar lantarki ba tare da wani kaykkyawan sakamako ba. Farfesan ya bayyana.

Sannan ya kara da, “Obasanjo Mutum ne da baya girmama kansa, saboda har kullum ji yake tamkar shi ne zai cigaba da shugabantar kasar nan har abada, kullum aikinsa shi ne zagin wadanda suka gaje shi don kawai yana kishin matsayinsu.”

KU KARANTA: Zambar N950m: Hukumar EFCC ta garkame Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau

“A saboda haka ina ganin ya kamata a taka masa birki, yasan cewa kyaleshi kawai aka yi. Maganar da shugaba Buhari yayi dai-dai ya fada kuma zai cigaba da fada tunda shi Obasanjon ya jagoranci Gwamnatin da take daya daga ckin wadda tafi kowacce cin hanci.”

Zazzafan martini ga Obasanjo: Gwamnatinka na daga cikin waddatafi cin hanci da rashawa - Sagay

Zazzafan martini ga Obasanjo: Gwamnatinka na daga cikin waddatafi cin hanci da rashawa - Sagay

Da yake amsa tambayar ko da akwai yiwuwar a binciki Obasanjon kan maganar wutar lantarki, Sagay cewa yayi, “Abu ne mai yiwuwa amma ban jin hakan zata faru. Sai dai za’a iya bincikarsa kan wasu badakaloli kamar yadda akai ya samu kudin da ya gina babban dakin karatunsa da kudin kamfanin kayan Motocinsa da kuma wasu makudan kudade da ya bayar cin hanci domin zarcewarsa da sauransu.”

Mutane dai da yawa sunyi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbata ya sanya an binciki tsohon shugaban kasar daga ciki akwai: Babban Lauya Chief Emeka Ngige (SAN) da tsohon shugaban kungiyar Lauyoyi ta kasa Dr. Olisa Agbakoba (SAN), da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel