Jagoran ‘Yan Neja-Delta ya zari takobin kare kuri’un Buhari a 2019

Jagoran ‘Yan Neja-Delta ya zari takobin kare kuri’un Buhari a 2019

- Wani Tubabben Tsageran Neja-Delta ya soki mulkin Jonathan

- ‘Dan Tawayen a-da ya kuma yabi Gwamnatin Shugaba Buhari

- Lawson yace Shugaba Buhari yayi aikin da har Jonathan ya gaza

Yayin da zaben 2019 yake kara kusantowa kusa mun samu labari daga Jaridar Leadership cewa wani tsohon Tsagera a Yankin Neja da ake kira Janaral Emma Lawson Sinaman yace za su kare kuri’un Shugaban kasa Buhari a Yankin.

Jagoran ‘Yan Neja-Delta ya zari takobin kare kuri’un Buhari a 2019

Wasu 'Yan Neja-Delta sun ce Buhari yayi aikin da Jonathan bai yi ba

Emma Lawson wanda aka fi sani da Janar yace za su tsaya tsayin-daka domin ganin babu wanda yayi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari coge a zabe mai uwan. Emma Lwason yace aikin da Shugaba Buhari yayi ya fi karfin a kirga.

KU KARANTA:

Tsohon ‘Dan Tawayen na Neja-Delta yace aikin da Shugaban Kasa Buhari yayi wa Yankin na su ya fi abin da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan yayi cikin shekaru 5 a mulki a Yankin da ke da arzikin fetur duk da cewa daga Kasar ya fito.

Janar Sinaman ya fadawa Duniya cewa ko sama da kasa za su hade sai ya kawowa Shugaba Buhari kuri’a kuma zai yi bakin kokarin sa wajen ganin babu wanda ya murde zaben. Sinaman yace ba za a yafewa duk wanda ya kawowa Buhari cikas ba.

Wannan tsohon ‘Dan Tawaye yace zai jagoranci Jama’ar sa su yi aikin ganin Buhari ya zarce a 2019 kuma babu wanda ya isa ya taka masu burki. Yace daga cikin aikin Gwamnatin Buhari akwai tada Jami’ar Maritime da wasu ayyuka na gani-a kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel