Gwamnatin Shugaba Buhari ta na biyan wadanda ke cikin kunci N5000 a Kwara

Gwamnatin Shugaba Buhari ta na biyan wadanda ke cikin kunci N5000 a Kwara

- Wasu Bayin Allah na amfana da Gwamnatin Shugaba Buhari

- A kan biya wasu da ke cikin halin matsi kudi N5000 duk wata

- Shugaba Buhari dai yayi alkawarin inganta rayuwar Talakan

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kawo wani tsari na biyan wadanda su ka fi kowa galabaita a Kasar nan kudi har N5000 a kowane wata domin raba su da matsi kamar yadda yayi alkawari.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta na biyan wadanda ke cikin kunci N5000 a Kwara

Ana biyan wasu fakirai N5000 duk wata a Gwamnatin Buhari

Mun samu labari daga wata Jami’ar wannan tsari na Gwamnatin nan cewa sama da mutane 14, 000 ne ke karbar kudin da Gwamnatin nan ta Shugaba Muhammadu Buhari ta ke biyan wadanda su ka fi kowa tagayarra a cikin Jihar Kwara

KU KARANTA:

Aminah Yahaya wanda ita ce Shugabar CCT ta Jihar Kwara tayi hira da manema labarai inda tace mutane sama da 14000 daga Kauyuka 480 na Kananan Hukumomi kusan 16 na Jihar ke amfana da wannan tsari da Shugaba Buhari ya kawo.

Yahaya tace Gwamnatin Shugaba Buhari na kokarin kara yawan masu samun wannan kudi su na kwance har gida. Wasu dai yanzu sun fara kananan kasuwanci da sana’a da wannan kudi da su ke samu daga Gwamnatin Tarayya inji Aminah Yahaya.

Kwanaki kun ji cewa Gwamnan Anambra Willie Obiano ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari ta na biyan Dattawa 3,086 daga Kananan Hukumomi kusan 6 Jihar kudi har N10, 000 a kowane wata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel