Yansandan Najeriya sun yi caraf da wasu gagga gaggan masu garkuwa da mutane su 14

Yansandan Najeriya sun yi caraf da wasu gagga gaggan masu garkuwa da mutane su 14

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da cafke wasu gagga gaggan yan fashi da makami su goma sha hudu, 14, da suka yi kaurin suna wajen tare babbar hanyar Kaduna zuwa Kano, inda suke satar mutane da nufin yin garkuwa dasu.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansanda, Jimoh Moshood ne ya sanar da haka a ranar Laraba 23 ga watan Mayu, inda yace gungun yan fashin ne suka kashe ani malami a jami’ar jihar Nassarawa, Dakta Ibrahim Mailafiya akan hanyar Kaduna zuwa Kano.

KU KARANTA: Hankaka maida Dan wani naka: Wani Gwamna ya zama Uba ga wani zakakurin Yaro

Bayan kisan Malamin ne babban sufetan Yansanda, Ibrahim Idris ya umarci kaddamar da bincike na karkashin kasa don kamo masu hannu cikin kisan, inda a tsakanin ranar 2 zuwa 23 na watan Mayu Yansanda na musamman suka kama yan fashin gaba dayansu.

Yansandan Najeriya sun yi caraf da wasu gagga gaggan masu garkuwa da mutane su 14

Miyagun

Kaakakin ya bayyana abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindigu guda 3, alburusai, motocin hawa da kuma wayoyin sata guda biyu, ciki har da na marigayi Mailafia. Sa’anan ya bayyana sunayensu kamar haka:

I. Sunday Jatau

II. Solomon Jatau

III. Ayuba Jatau

IV. Ishaku Luka

V. Ibrahim Daniel

VI. Emmanuel Garba

Yansandan Najeriya sun yi caraf da wasu gagga gaggan masu garkuwa da mutane su 14

Miyagun

VII. Alhaji Usman Mohammed

VIII. Alhaji Ibrahim Baba

IX. Bello Aliyu

X. Surajo Mohammed

XI. Hassan Ibrahim

XII. Bature Adamu

XIII. Bello Abdullahi

XIV. Mamuda Mohammed

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel