Gwamnatin Obasanjo na daya daga cikin mafi shahara akan Rashawa - Sagay

Gwamnatin Obasanjo na daya daga cikin mafi shahara akan Rashawa - Sagay

A ranar Larabar da ta gabata ne Farfesa Itse Sagay, jagoran kwamitin bayar da shawarwari akan dakile rashawa ga shugaban kasa ya bayyana cewa, gwamnatin tsohon shugaban kasa Obasanjo na daya daga cikin mafi shahara akan rashawa a tarin kasar nan ta Najeriya.

Yake cewa, Obasanjo ya na da halayya irin ta mumminin kare mai ladabin kunama, wanda a hakikanin gaskiya babu mutum mafi kashi a tattare da gindin sa.

A yayin tuntubar babban lauyan dangane da cancantuwar titsiye tsohon shugaban kasar akan Dalar Amurka Biliyan 16 da ya batar a bangaren wutar lantarki ba tare da wani abin zo a gani da hakan ya haifar ba, Sagay yace tabbas hakan ya dace da daidai.

A kalaman sa, "shugaba Buhari ya kasance mai karamci da dattako yayin mu'amalantar magabantan shugabanni a sanadiyar rashin son haifar masu da rashin jin dadi ko kunya a gare su sakamakon nauyin kujerar da suka rike."

Itse Sagay

Itse Sagay

"Sai dai Obasanjo mutum ne da ba ya rike girman sa wanda ya ke tunanin shine shugaban kasar Najeriya da yake saman kowa da a koda yaushe yake kutsa kansa cikin lamuran da basu shafe sa ba ta hanyar cin fuskar wadanda suka gaji kujerar sa don kurum yana bakin cikin mukamin da suke rike da shi."

"Ya kamata a dauki mataki a kansa domin kuwa ganin damar da yake yi a kasar nan ya kai makura."

KARANTA KUMA: Mutane 3 dauke da Cutar Ebola sun gudu daga Asibiti a Kasar Congo

"Dangane da batun shugaba Buhari akan rikon sakainar kashi da aka yi wajen batar da $16m na gyaran wutar lantarki babu shakka yana tattare da kamshin gaskiya sakamakom irin mulkin kama karya na Obasanjo wanda yana daya daga cikin mafi shahara ta fuskar rashawa a tarihin Najeriya."

A yayin haka kuma, wasu daga cikin manyan lauyoyi a kasar nan sun yi kira dangane da fara gudanar da bincike akan kudaden wutar lantarki da suka salwanta a gwamnatin Obasanjo ba tare da la'akari da wadanda abin ya shafa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel