Zambar N950m: Hukumar EFCC ta garkame Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau

Zambar N950m: Hukumar EFCC ta garkame Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau

Mun samu rahoton cewa, hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa watau EFCC, ta garkame tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Shekarau a ranar yau ta Laraba a reshen ta na jihar Kano tare da wasu biyu da ake tuhuma da laifin zamba.

Hukumar ta garkame tsohon gwamnana tare da tsohon ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Aminu Wali da kuma Engr. Mansur Ahmad, jagoran Arewa akan yakin neman zabe na tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar ta garkame jiga-jigan na kasar nan sakamakon zargin su da aikata laifi zambar makudan kudade ta kimanin Naira Miliyan 950 tun a shekarar 2015 da ta gabata.

Zambar N950m: Hukumar EFCC ta garkame Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau

Zambar N950m: Hukumar EFCC ta garkame Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Nation sun bayyana cewa, hukumar ta gayyaci wadannan mutane uku a ranar Talatar da ta gabata inda ta titsiye su har na tsawon sa'a guda bisa zargin aikata zambar N950m cikin kudin zabe na shekarar 2015.

KARANTA KUMA: Wani Matashin Malami ya yi lalata da 'Dalibar sa 'Yar shekara 4 a jihar Neja

Sai dai a ranar yau ta Laraba, hukumar ta sake aika sammaci akan shugabannin uku, inda ta garkame su har zuwa wayewar gari na gobe Alhamis inda za a gurfanar da su gaban babbar kotun tarayya dake jihar Kano.

Ana zargin tsohon gwamnan na jihar Kano da yin sama da fada da kimanin Naira Miliyan 25 cikin wannan kaso na N950m, inda a halin yanzu zasu shafe daren yau na Alhamis a katarar hukumar ta EFCC wadda ta tsananta tsaro sabanin yadda ta saba yau da kullum.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel