Okonjo Iweala tayi wa kasashen Afirka kashedi kan kwaikwayon China a fannin tattalin arziki

Okonjo Iweala tayi wa kasashen Afirka kashedi kan kwaikwayon China a fannin tattalin arziki

- Lasashen Afirla na kallon kasar China a matsayin abar koyi

- Sai dai suna bin tsarin gurguzu ne, maimakon jari hujja

- Okonjo Iweala tayi karin haske ta kuma bada shawara

Okonjo Iweala tayi wa kasashen Afirka kashedi kan kwaikwayon China a fannin tattalin arziki

Okonjo Iweala tayi wa kasashen Afirka kashedi kan kwaikwayon China a fannin tattalin arziki

Kasar China ta fitar da biliyoyin daloli don taimako, bashi da kuma kasuwanci ga Nahiyar Afirka a cikin shekarun nan.

Amma duk da zumunci ya cigaba da karfi, tsohuwar ministan kudi, Ngozi Okonjo Iweala ta yi gargadi da cewa yanayin tsarin tattalin arziki na Beijing ba zai ma Afirka aiki ba.

"China dai tana taimako, balle gurin tabbatar da ababen more rayuwa a Afirika." Tsohuwar ministan kudin ta fadawa CNBC

Amma kasashen da suke da cigaban tattalin arziki da basu kai kasar China ba zasu yi burin kwaikawayon nasarar cigaban tattalin arzikinta, to yanayin ba zai dace da mafi yawancin kasashen Afirka.

"A kasashen Afirka da yawa, yanayin na tattalin arzikin nasu beyi musu amfani ba." Okonjo Iweala tace.

DUBA WANNAN: Iyayen wani gardi sun kai qara don dansu ya ki girma da zama gida

Ta bada misali da kasar Najeriya "Kwazon bangarori masu zaman kansu ba zai kai ta ga mafita ba,balle ta bangaren masana'antu manya, masu sarrafawa. Wasu daga cikin gwamnatocin mu in aka basu damar samarda aiyuka, a nan rashawa take samun hanyar shigowa."

Okonjo Iweala dai tayi ministan kudi a Najeriya har sau biyu, daga 2003-2006, da kuma 2011-2015 a karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Tsohuwar darakta ce a bankin duniya, yanzu kuma mai bada shawara ce ga Asian Infrastructure Development Bank.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel