An bukaci Shugaba Buhari ya cinnawa Obasanjo da Jonathan hukumar EFCC

An bukaci Shugaba Buhari ya cinnawa Obasanjo da Jonathan hukumar EFCC

Wata kungiya mai zaman kanta a Najeriya dake rajin kare martabar dan adam da kuma tabbatuwar demokradiyya watau Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) a turance ta bukaci gwamnatin tarayya da ta soma binciken tsaffin shugabannin kasar Najeriya game da yadda suka tafiyar da harkar wutar lantarkin kasar.

SERAP a cikin wata sanarwa da ta fitar ta rabawa manema labarai, ta bayyana cewa abun takaici ne a kashe kusan dalar Amurka biliyan 16 a harkar wutar lantarkin amma har yanzu ba ta canza zane ba.

An bukaci Shugaba Buhari ya cinnawa Obasanjo da Jonathan hukumar EFCC

An bukaci Shugaba Buhari ya cinnawa Obasanjo da Jonathan hukumar EFCC

KU KARANTA: Mista Taiwo - dattijon da ya kirkiro tutar Najeriya

Legit.ng ta samu cewa kungiyar daga nan ne ta shawarci shugaban kasar da ya mika tsaffin shugabannin kasar ga hukumomin bincike da ya kamata domin gudanar da bincike a kan su.

A wani labarin kuma, Hukumar nan dake yaki da cin hanci da rashawa ta gwamnatin tarayya watau EFCC ta tasa keyar babban sakataren gwamnatin jihar Ribas mai suna Mista Kenneth Kobani tare da wani dan siyasa a jihar mai suna Samuel Okpoko zuwa kotu bisa zargin laifuka 6.

Kamar dai yadda muka samu, cikin laifukan da ake tuhumar mutanen hadda kuma laifin karbar kudin haram da suka kai Naira miliyan 750 daga hannun tsohuwar ministar man fetur a lokacin gwamnatin da ta gabata ta Goodluck Jonathan Diezani Alison- Madueke.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel