An gurfanar da dan Atiku a gaban kotu saboda ya gaza biyan alawus din 'ya'yan sa

An gurfanar da dan Atiku a gaban kotu saboda ya gaza biyan alawus din 'ya'yan sa

A yau Laraba ne wata babban kotu da ke zamanta a Igbosere jihar Legas ta saurari karar da aka shigar a kan, Aminu Atiku, dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar saboda rashin biyan kudin kulawa da yaransa N250,000 duk wata da bai biya ba tun watan Fabrairun 2018.

Sai dai Aminu Atiku ya shaidawa Alkali kazeem Alogba cewa yana daukan dawainiyar duk bukatu na yaransa.

A yau din Alogba zai zartas da hukunci a kan wata bukata da Atiku ya shigar a kotun inda ya ke rokon a janye kudin wata na kulawa da yaran da kotu ta gindaya masa a baya.

KU KARANTA: Daga yanzu laifi ne aurar da macen da bata haura shekaru 18 ba - Gwamnatin jihar Borno

Kotun ta tsayar da rannan zartas da hukuncin ne bayan jin muhawarrar da lauyan Atiku, Oyinkan Badejo da kuma Ethel Okoh, lauyan tsohuwar matarsa, Ms Ummi Fatima Bolori suka tafka.

Atiku da tsohuwar matarsa Bolori duk basu samu hallartan kotun ba.

A karar da ya shigar, Atiku yana rokon kotun ta canja hukuncin da wata kotun ta zartar a baya inda aka dankawa tsohuwar matar rainon yaransu Ameera mai shekaru 11 da kuma Aamir mai shekaru 7.

Da aka fara sauraron karar a yau Laraba, Badejo ta bayyana cewa akwai alamar tambaya a kan biyan N250,000 a kowanne wata da aka daura wa Atikun duk da cewa yana daukan nauyin dawainiyar yaran.

A cewarta, Atikun yana dauke dukkan nauyin yaransa wanda suka hada da biyan kudin makarantarsu tare da kudin magani da sauransu.

Lauyan ta ce kotun da ta yanke wannan hukuncin ba ta yi la'akari da karfin aljihun Atikun ba shiyasa ta daura masa N250,000 a duk wata, ta kara da cewa bai dace ayi la'akari da dukiyar da iyayen Atikun suka mallaka ba.

Sai sai Lauyan Bolori, Okoh ta kallubalanci wannan zancen. Ta ce tun da Atikun bai biya kudin kulawa da yaran ba tun watan Maris, inda ta kara da cewa rashin biyan kudin kulawa da yaran ya sabawa sashi na 62(5) na dokar kiyaye hakkin yara.

Ta yi ikirarin cewa Atiku bai biya kudin makarantar yaransa ba sai ranar 11 ga watan Afrilu, kwana daya kafin kotun ta saurari karar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel