Almundahanar N750 miliyan: EFCC ta tasa keyar Sakataren gwamnatin jihar Ribas zuwa kotu

Almundahanar N750 miliyan: EFCC ta tasa keyar Sakataren gwamnatin jihar Ribas zuwa kotu

Hukumar nan dake yaki da cin hanci da rashawa ta gwamnatin tarayya watau EFCC ta tasa keyar babban sakataren gwamnatin jihar Ribas mai suna Mista Kenneth Kobani tare da wani dan siyasa a jihar mai suna Samuel Okpoko zuwa kotu bisa zargin laifuka 6.

Kamar dai yadda muka samu, cikin laifukan da ake tuhumar mutanen hadda kuma laifin karbar kudin haram da suka kai Naira miliyan 750 daga hannun tsohuwar ministar man fetur a lokacin gwamnatin da ta gabata ta Goodluck Jonathan Diezani Alison- Madueke.

Almundahanar N750 miliyan: EFCC ta tasa keyar Sakataren gwamnatin jihar Ribas zuwa kotu

Almundahanar N750 miliyan: EFCC ta tasa keyar Sakataren gwamnatin jihar Ribas zuwa kotu

KU KARANTA: Karanta yadda karuwai 'yan Najeriya ke rayuwa a Turai

Legit.ng ta samu cewa kudaden dai na daga cikin kudaden da aka ware domin baiwa jami'an hukumar zabe cin hanci domin a murde zaben na 2015.

A wani labarin kuma, Wata kungiya mai zaman kanta a Najeriya dake rajin kare martabar dan adam da kuma tabbatuwar demokradiyya watau Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) a turance ta bukaci gwamnatin tarayya da ta soma binciken tsaffin shugabannin kasar Najeriya game da yadda suka tafiyar da harkar wutar lantarkin kasar.

SERAP a cikin wata sanarwa da ta fitar ta rabawa manema labarai, ta bayyana cewa abun takaici ne a kashe kusan dalar Amurka biliyan 16 a harkar wutar lantarkin amma har yanzu ba ta canza zane ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel