Baitul malin Najeriya ya kai $47 biliyan - Shugaba Buhari

Baitul malin Najeriya ya kai $47 biliyan - Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a jiya ya bayyana cewa kawo yanzu kudaden ajiya na kasashen waje ko baitulmalin Najeriya ya kai akalla $47 biliyan tun 9 gawan Afrilu sabanin $29.6 biliyan din da suka samu kasar a watan Mayu na shekarar 2015.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron karrama wasu zakakuran Najeriya na rukunin National Productivity Order of Merit (NPOM) a turance da ya gudana a garin Abuja.

Baitul malin Najeriya ya kai $47 biliyan - Shugaba Buhari

Baitul malin Najeriya ya kai $47 biliyan - Shugaba Buhari

KU KARANTA: Dattijan Najeriya 4 da suka shawarci Buhari kar ya tsaya takara a 2019

Legit.ng ta samu cewa shugaban ya bayyana hakan a matsayin wani gagarumin cigaba da aka samu a kasar sannan kuma ya bukacin dukkan ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa da su maida hankali sosai wajen ganin kasar nan ta cigaba.

A wani labarin kuma, Shehunnan malaman addinin kirista a Najeriya jiya sun bukaci shugaban kasar Najeriya da yayi murabus ko kuma ya tabbatar da samar da kyakkyawan tsaron da zai ba jama'ar kasar nan kariya daga kashe-kashe.

Babban Rabaran din Dakta Martin Uzoukwu da yayi magana a madadin sauran 'yan uwan sa yayin wani gangamin nuna rashin jin dadi game da kisan 'yan uwan su manyan malamai a jihar Benue ya bayyana cewa ba za su lamunci cigaba da kisan na su ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel