Abinda muka tattauna da shugabannin hukummomin tsaro a yau – Saraki

Abinda muka tattauna da shugabannin hukummomin tsaro a yau – Saraki

A yau ne aka yi wata tattaunawa a majalisar dattijai tsakanin shugabannin hukumomin tsaro da mambobin majalisar a kan shigar makamai hannun farar hula da kuma batun kashe-kashe a wasu jihohin Najeriya.

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar karanci da rashin wadatattun kudade ga hukumomin tsaro na daga cikin abubuwan da suka bawa muhimmanci yayin tattaunawar ta su.

A cewar Saraki, dukkan bangarorin biyu sun amince za a kirkiri wata doka ta musamman cikin sati biyu masu zuwa domin samar da isassun kudade ga hukumomin tsaron kasar nan.

Abinda muka tattauna da shugabannin hukummomin tsaro a yau – Saraki

Abinda muka tattauna da shugabannin hukummomin tsaro a yau – Saraki

Kudin da ake saka ran bawa hukumonin tsaron a matsayin kari zai zo ne cikin kunshin bukatu na musamman. Karin kasafin kudin daban yake da bukatar shugaba Buhari na kashe wata Karin dalar Amurka biliyan $1bn a kan tsaro day a aikewa majalisar.

DUBA WANNAN: Wayyo: Duba yadda shahararren jarumin fim Jet Li ya koma bayan gamuwa da wata cuta

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Abayomi Olonisakin, da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Lawal Daura, na daga cikin wadanda suka halarci taron.

A larabar makon jiya ne majalisar ta dattijai ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro domin tattauna matsalar rigingimu masu nasaba da kabilanci da suka mamaye wasu sassan kasar nan. Kazalika majalisar ta gayyaci shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali, domin ya yi mata bayani a kan kwararowar makamai cikin Najeriya daga kasashen ketare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel