Har yanzu kasafin kudin 2018 bai shigo hannun shugaban kasa ba – Ministan kasafin kudi

Har yanzu kasafin kudin 2018 bai shigo hannun shugaban kasa ba – Ministan kasafin kudi

Mako daya bayan majalisan dattawa da na wakilai sun tabbatar da kasafin kudin 2018, har yanzu bai shiga hannun shugaba Buhari domin rattaba hannu ba.

Wannan labari ya fito ne daga bakin ministan kasafin kudi da shirye-shirye, Udo Udoma, yayinda yake amsa tambayoyin yan jarida bayan ganawar majalisar zantarwa a yau Laraba, 23 ga watan Mayu, 2018.

Mista Udoma ya karyata rahotannin da ke cewa shugaba Buhari y ace ba zai rattaba hannu kan kasafin kudin ba.

Yace: “Shugaban kasa ba karbi kasafin kudin ba. Saboda haka ba zai yiwu inyi magana akan kasafin kudi da ba’a kawo ba tukun. Idan ya shigo hannunmu, zamu yi aiki kanshi ba tare da bata lokaci ba."

Har yanzu kasafin kudin 2018 bai shigo hannun shugaban kasa ba – Ministan kasafin kudi

Har yanzu kasafin kudin 2018 bai shigo hannun shugaban kasa ba – Ministan kasafin kudi

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika samfurin kasafin kudin 2018 ga gamayyar majalisan dattawa da na wakilai ranan 7 ga watan Nuwamba, 2017 amma basu tabbatar da shi ba sai ranan 16 ga watan Mayu, 2018.

Yan majalisan sun kara kudin daga N8.6 trillion zuwa N9.1 trillion, bayan ya kwashe wattani 6 a hannunsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel