Mutane 3 dauke da Cutar Ebola sun gudu daga Asibiti a Kasar Congo

Mutane 3 dauke da Cutar Ebola sun gudu daga Asibiti a Kasar Congo

Mun samu rahoton cewa, wasu mutane uku masu dauke da cutar na ta Ebola sun sulale daga kebetaccen reshe na wani asibitin dake birnin Mbandaka a kasar Congo.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa, wata cibiyar agaji ce dake birnin na Mbandaka ta bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata.

Shugaban cibiyar Henry Gray, ya bayyana cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne wasu marassa lafiya dauke da cutar ta Ebola suka sulale daga cibiyar lafiya ta Medecin Sans Frontieres dake birnin, inda aka samu nasarar damko washe garin ranar ta Talata.

Wakilin cibiyar lafiya ta duniya dake reshen na kasar Congo, Yokouide Allarangar, ya bayyana cewa an tsinto daya daga cikin mutane biyun ne bayan ajali ya katse masa hanzari, inda aka sake mayar da cikon gudan asibiti wanda bayan wasu 'yan lokuta shima rai ya yi ma sa hali.

Mutane 3 dauke da Cutar Ebola sun gudu daga Asibiti a Kasar Congo

Mutane 3 dauke da Cutar Ebola sun gudu daga Asibiti a Kasar Congo

A yayin ganawa da manema labarai a babban birnin kasar na Kinshasha, Allarangar ya bayyana cewa marasa lafiyan biyu sun samu nasarar tserewa ne daga asibitin da taimakon wani dan uwan nasu, inda suka garzaya wani dakin bauta domin rokon addu'o'i.

KARANTA KUMA: 'Yan ta'adda 700 na Boko Haram sun shirya saduda - Gwamnatin Najeriya

Kamar yadda shafin jaridar Reuters ya bayyana, wani mutum mai dauke da cutar ta Ebola ya ari kafar kare daga wani asibiti a kasar a ranar Asabar din da ta gabata inda daga bisani sai dai gawar sa aka tsinto.

Rahotannin sun bayyana cewa, cibiyar lafiya ta kasar ta bayar da umarni ga hukumomin tsaro akan dakile afkuwar hakan a lokuta ne gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel