Ka daina surutai, Afenifere sun caccaki Buhari

Ka daina surutai, Afenifere sun caccaki Buhari

Kungiyar yan kabila Yoruba, Afenifere, a jiya Talata sun baiwa shugaba Buhari shawara ya daina surutai, yan Najeriya sun gashi da surutai.

Kakakin kungiyar, Yinka Odumakin, ya bayyana haka ne a wani hira da yayi da jaridar The Punch yayinda yake tofa albarkin bakinshi kan sukan shugaba Buhari yayiwa Obasanjo.

Ya bukaci Buhari ya shawo kan yan majalisa tun shawancin yan majalisan yan jam’iyyar APC ne.

“Yan Najeriya sun gaji da surutansa. Ya tashi yayi aiki. Idan yana kukan cewa majalisan dokoki basuyi komai ba shekaru 10 da suka wuce, shi me ya tsinana a shekaru 3 da suka gabata?

A tunani na mun gaji da kukunai. Ya mike tsaye yayi aiki. Rayukan mutane ya zama banza a kasan nan; ana kashe mutane Kaman kaji,” Odumakin yace.

Ka daina surutai, Afenifere sun caccaki Buhari

Ka daina surutai, Afenifere sun caccaki Buhari

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya mayar da martani da shugaba Muhammadu Buhari akan zargin almubazzarancin $16 billion kan samar da wutan lantarki.

A wani jawabin ya mai magana da yawun Obasanjo, Kehinde Akinyemi, ya saki, ya ce shugaba Muhammadu Buhari yayi magana a kan jahilci.

Yayinda ya karbi bakuncin magoya bayansa a fadar shugaban kasa a yau Talata, shugaba Buhari yace tsohon shugaban kasa ya amsa tambayoyi a kan kudaden.

KU KARANTA: Rikicin Boko Haram ya jefa rayuwar Mutane Miliyan 14.8 cikin mawuyacin hali

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel