An kira ‘Yan Sanda da sanyin safe a Amurka saboda kai kukan alade

An kira ‘Yan Sanda da sanyin safe a Amurka saboda kai kukan alade

- Wani Bawan Allah ya kira Jami’an tsaro da asuba yana karar wani alade

- ‘Yan Sanda sun yi tunani wannan mutumin yana cikin buguwar giya ne

- Ko da Jami’an tsaro su ka zo sun iske aladen ya tasa wannan mutumi gaba

Mun samu labari cewa an wayi Gari a Amurka wancan makon da ya gabata da abin al’ajabi inda wani mutumi ya kira ‘Yan Sanda cikin sanyin safiya domin su raba shi da wani jarababben alade.

Kamar yadda mu ka samu labari daga BBC Hausa, wannan mutumi dai ya ba ‘Yan Sandan Jihar Ohio a Kasar Amurka mamaki inda ya tuntube su a waya yana mai kawo kukan wani alade da ya hana shi sakat tun karfe 5:30 na asuba.

Labari ya zo mana cewa Jami’an ‘Yan Sandar sun yi tunani cewa wannan Bawan Allah da ya kwala masu kira cikin safe ya zautu ne ko kuma ya na cikin maye. Sai dai ta tabbata cewa aladen ya biyo wannan mutumi ne zuwa gidan sa.

Ko da Jami’an ‘Yan Sanda su ka isa gidan wannan mutumi sais u ka iske sa kalau ba kamar yadda su kayi tunani ba. ‘Yan Sandan na Yankin Arewacin Garin Ridgeville sun dauke aladen sun kuma maida shi zuwa ga mai shi a Jihar ta Ohio.

Yan Sanda sun shiga tsakanin wani Mutumi da alade a Amurka don kuwa 'Yan sanda sun saba da samun kira daga wajen jama'a, amma kiran da wani mutum ya yi musu a wata safiyar Asabar ta sa sun iske alade ya tasa wani mutumi a gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel