Ba kanta: Kwalara ta barke a jihar Adamawa har Mutane 12 sun Mutu

Ba kanta: Kwalara ta barke a jihar Adamawa har Mutane 12 sun Mutu

Akalla Mutane 12 suka Mutu sakamakon barkewar Kwalara a jihar Adamawa dake Arewa masu Gabashin Najeriya.

Daraktan shashin bayar da agajin gaggawa na jihar Dr Bwalki Dili ne ya bayyana hakan yau Laraba cewa a kalla Mutane 142 ne suka kamu bayan barkewar kwalaral.

Ba kanta: Kwalara ta barke a jihar Adamawa har Mutane 12 sun Mutu

Ba kanta: Kwalara ta barke a jihar Adamawa har Mutane 12 sun Mutu

“Mun samu alkalumman da suka nuna cewa Mutane 12 sun Mutu cikin kwana hudu da suka gabata, kuma wasu 142 sun kamu tun bayan barkewar kwayar cutar. Amma hukuma ta dauki matakin rarraba magani da kuma tura jami’an lafiya domin bayar da agajin gaggawa don shawo kanta.” Amma sai dai har ya zuwa yanzu ba’a kai ga gano musabbabin bullar cutar ba. A cewar Dilli.

KU KARANTA: Bafarawa ya yi bude baki da limamin Makka, Sheikh Sudais (hotuna)

Cutar Kwalara dai ana samunta ne a cikin abinci maras tsafta ko kuma gurbataccen ruwan sha wanda hakan kan haifar da gudawa ba kakkautawa. Kuma yara sun fi zama cikin hadari kasancewar garkuwar jikinsu na da rauni.

Ba kanta: Kwalara ta barke a jihar Adamawa har Mutane 12 sun Mutu

Ba kanta: Kwalara ta barke a jihar Adamawa har Mutane 12 sun Mutu

Asali dai rashin tsafta ne yake haifar da yawancin cututtukan da ake dauka a ruwa musamman yayin da aka fara ruwan sama, domin yakan kwashi datti ya kais u wurin da ruwa yake tare wuri daya wanda watakila shi jama’ar yankin kan amfani da shi wajen sha da aiyukan gida.

Ko a watan da ya gabata ma a jihar Yobe wadda makwabciyar jihar ta Adamawa ce an samu Mutuwar wasu Mutane 13 a dalilin barkewar cutar ta kwalara wanda mazauna yankin suka ga baiken mahunkuntan yanki wajen rashin tsaftataccen ruwan sha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel